Gwamnatin jihar Nassarawa tace zataci gaba da taimakawa 'yan gudun hijira

Gwamnatin jihar Nassarawa tace zataci gaba da taimakawa 'yan gudun hijira

- 'Yan gudun hijira daga jihar Benuwe sun kwarara a garin Tunga dake jihar Nasarawa

- Gwamnan jihar Nasarawa yace sun kashe kudi har sama da naira miliya 50 wajen agazawa 'yan gudun hijira

Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce zata cigaba da taimakawa ‘yan gudun hijira daga jihar Benuwe.

Yanzu haka dubban ‘yan gudun hijira daga jihar Benuwe sun kwarara a garin Tunga dake karamar hukumar Awe a jihar Nasarawa.

Yawancin yan gudun hijiran yan kabilar Tiv ne da suka gudu daga gidajen su saboda tsoron kada rikici ya kara rutsa wa da su.

Gwamnatin jihar Nassarawa tace zataci gaba da taimakawa 'yan gudun hijira

'Yan gudun hijira daga Benuwe

Shugaban kungiyar raya al’ummar garin, Tunga Alhaji Saidu Mohammad, ya bukaci gwamnati ta dama masu hannu da shuni wajen cigaba da taimakwa mutanen da suka gudu daga garin su.

KU KARANTA : Buhari zai ziyarci Benue, da Sauran wuraren da akayi Kashe kashe – Adesina

Gwamnan jihar ta Nassarawa yace sun kashe kudi har sama da naira miliya 50 domin agazawa 'yan gudun hjiran, kuma ba zasuyi kasa a gwiwa wajen tabbatar da inganta matakan tsaro a yankin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel