2019: Karyan makiya, Ina nan daram a APC – In ji wani dan majalisa

2019: Karyan makiya, Ina nan daram a APC – In ji wani dan majalisa

- Wani dan majalisar dokokin jihar Ogun ya ce makiyansa na masa fatar ficewa daga APC

- Dan majalisar ya ƙaryata labarin cewa ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP

- Odofin-Sonuga ya bayyana cewa ba shi da wani dalili na yin watsi da APC ga wata ƙungiyar siyasa

Wani dan majalisar dokokin jihar Ogun, Hon. Olusola Odofin-Sonuga, a ranar Talata, 16 ga watan Janairu, ya ƙaryata labarin da ke yawo a kafofin yada labarai cewa ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

Odofin-Sonuga, wanda ke wakiltar mazabar Ikenne, ya bayyana hakan ne a Abeokuta babban birnin jihar, cewa ba shi da wata matsala da jam'iyyarsa, APC.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, dan majalisar ya ce ba shi da wani dalili na yin watsi da APC ga wata ƙungiyar siyasa.

2019: Karyan makiya, Ina nan daram a APC – In ji wani dan majalisa

Dan majalisar dokokin jihar Ogun, Hon. Olusola Odofin-Sonuga

"Game da labarai masu ban mamaki da ke yawo a tsakanin jama'a cewa na koma PDP. Wannan ba gaskiya bane kuma yana da muhimmanci in warware matsalar nan da nan”.

KU KARANTA: Yan majalisu sun wasa wukarsu don bincikar dala miliyan 44 da suka ‘ɓace’ a hukumar liken asiri

"A makon da ya wuce, na ziyarci Ladi Adebutu, dan majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar PDP a gidansa da ke Iperu Remo, jihar Ogun”.

"Na ziyarce shi don na yi masa jaje game da mummunar hatsarin wuta da ya faru a gidansa, amma abin mamaki, zai na samu labarai daga kafofin watsa labaru cewa na canza sheka, nan da nan na fara samun kira daban-daban don tabbatar maganar”.

"Ina so in tabbatar muku cewa akwai jiga-jigan APC da dama wadanda suka ziyarci Adebutu a wannan rana”, in ji shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel