Jami’an tsaro na sirri sun diran ma wani Malami da yayi kira da a kada Buhari a 2019

Jami’an tsaro na sirri sun diran ma wani Malami da yayi kira da a kada Buhari a 2019

Jami’an tsaro na sirri, DSS sun dira gidan wani malamin addinin Kirista bayan ya umarci mabiyansa da su tabbata su kayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabukan 2019.

Saura kiris wannan Fasto mai suna Isa El-Buba ya shiga hannun jami’an DSS a daren Litinin 15 ga watan Janairu, in ban da taimakon shugaban kungiyar addinin Kirista na Arewa ta tsakiya, Yakubu Pam.

KU KARANTA: Bango ya tsage: rikita rikita ta kunno kai a tsakanin manyan muƙarraban shugaban kasa

Premium Times ta ruwaito kadan ya rage a fafat tsakanin matasan unguwar da Faston ke zama a garin Jos da jami’an, sai dai Fasto Pam ya tabbatar da kasha wutan rikicin, inda yace yanzu hankula sun kwanta, ba tare da bayyana dalilin rikicin ba.

Jami’an tsaro na sirri sun diran ma wani Malami da yayi kira da a kada Buhari a 2019

Jami’an tsaro na sirri

Amma majiyar Legit.ng ta samu karn bayani daga wani makusancin Fasto El-Buba, wanda yace an yi kokarin kama Faston ne sakamakon batutuwan da yayi game da kashe kashen da aka yi a jihar Benuwe, wanda ya danganta shi da gazawa irin na shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Majiyar ta tabbatar da Faston yayi wannan zance ne ciki wani bidiyo, inda yayi kira ga mabiyansa dasu nemo Karin zabensu don su kayar da Buhari a zaben 2019 sakamakon kashe kashenn.

Daga karshe shugaban hukumar DSS na jihar Filato ya umarci Fasto Pam daya tattauna da Fasto El-Buba kuma ya kai masa rahoton yadda ganawar tasu kasance.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel