Yan majalisu sun wasa wukarsu don bincikar dala miliyan 44 da suka ‘ɓace’ a hukumar liken asiri

Yan majalisu sun wasa wukarsu don bincikar dala miliyan 44 da suka ‘ɓace’ a hukumar liken asiri

Majalisar wakilai a zamanta na ranar Talata 16 ga watan Janairu ta yanke shawarar bincike da jin kwakwaf kan musabbabin bacewar wasu makudan daloli da ake zargi a hukumar liken asiri ta kasa, NIA.

Rahotanni sun bayyana cewar ana zargin kudaden sun yi batan dao ne jim kadan bayan ranstar da sabon shugaban hukumar,Abubakar Ahmed Rufai, kamar yadda Legit.ng ta jiyo.

KU KARANTA: Bango ya tsage: rikita rikita ta kunno kai a tsakanin manyan muƙarraban shugaban kasa

Dayake jawabi yayin zaman majalisar, dan majalisa daga mazabar Yenagoa/Kolokuma/Opokuma na jihar Bayelsa, Doye Diri ya bayyana lamarin a matsayin abi takaici, inda ya bukaci a gudanar da bincike don tabbatar da gaskiyar lamarin.

Yan majalisu sun wasa wukarsu don bincikar dala miliyan 44 da suka ‘ɓace’ a hukumar liken asiri

Yan majalisa

Dayake tofa albarkacin bakinsa kan lamarin, dan majalisa daga jihar Enugu, Toby Okechukwu ya bayyana lamarin a matsayin abin kunya, inda yace wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da ke kokarin shawo kan badakalar data faru a hukumar, inda wasu dala miliyan 40 suka bace a baya.

Bayan kammala tattaunawar ne, sai Kaakakin majalisar, Yakubu Dogara ya umarci kwamitin majalsar dake sa ido kan ayyukan hukumomin tsaro na sirri data binciki gaskiyar lamarin, kuma ta bada rahotonta cikin sati biyu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel