Ganduje ya zantar da hukunci kan dakatarwar da aka yi ma jaruma Rahama Sadau

Ganduje ya zantar da hukunci kan dakatarwar da aka yi ma jaruma Rahama Sadau

Rahotanni sun kawo cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya dage dakatarwan da kungiyar kula da da’an masu shirya fina-finan Hausa ta MOPPAN ta yi wa Rahama Sadau.

Kungiyar yan wasan Hausa na jihar Kano ta yaba ma gwamna Ganduje bisa wannan mataki da ya dauka n adage takunkumin da aka sanya ma jarumar.

Shugaban kungiyar Alhaji Alhassan Kwalli bayyana cewa wannan matakin na da amfani matuka a daidai wannan lokaci da masana'antar fina-finai hausa ke kokari wajen samar da cigaba a kasar ta hanyar ayyukan ta.

Ganduje ya zantar da hukunci kan dakatarwar da aka yi ma jarumar Kannywood

Ganduje ya zantar da hukunci kan dakatarwar da aka yi ma jarumar Kannywood

A cikin takardar wanda mataimakin sakataren kungiyar Rabiu Rikadawa ya fitar a ranar litinin, yayi ma gwamnan godiya kan daga dakatarwar da aka yi ma Rahama Sadau.

KU KARANTA KUMA: An gurfanar da tsohuwar ministar Abuja da wasu 2 a jihar Lagas (hotuna)

Kungiyar ta kuma jinjina ma mai girma gwamna bisa goyon baya da yake baiwa masana'antar fina-finan hausa da ma jaruman cikin ta.

Idan dai ba zaku manta ba kungiyar MOPPAN ta dakatar da jaruma Rahama tun bayan fitowa da tayi a wani bidiyo na mawaki Classiq wanda ya saba ma dokar kungiyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel