Buhari zai ziyarci Benue, da Sauran wuraren da akayi Kashe kashe – Adesina

Buhari zai ziyarci Benue, da Sauran wuraren da akayi Kashe kashe – Adesina

- Femi Adesina ya ce shugaba Buhari zai zai ziyarci jihar Benuwe da sauran wuraren da aka yi kashe-kashe

- Adesina ya karyata zargin da ake yiwa shugaban kasa akan nuna halin koi’nkula game da kashe kashen da ake yi a kasar

Mai ba wa shugaban kasa shawara a fannin watsa labaru, Femi Adesina, ya bayyana dalilin da yasa Buhari bai ziyarci jihar Benuwe da sauran wuraren da aka yi kashe-kashe ba, amma zai ziyarci wuraren idan lokaci yayi.

femi Adeaina ya mayar wa da martani ga mutanen da suka ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya na nuna halin ko’inkula akan da ta’adancin da makiyaya suke yi a kasar .

Femi Adesina ya bayyana haka ne a hirar da yayi da gidan Talabijin na Channels a ranar Lahadi.

Buhari zai ziyarci Benue, da Sauran wuraren da kayi Kashe kashe – Adesina

Buhari zai ziyarci Benue, da Sauran wuraren da kayi Kashe kashe – Adesina

Adesina yace shugaban kasa ya umarci Sfeton janar na yansada ya koma jihar Benuwe da zama dan shawo kan matsalar, bayan haka ya kara tura Ministan harkan cikin gida, da rundunar sojoji jihar.

KU KARANTA : ‘Yan sandan Kano sun bada belin kwamishinan da ya ce a jefi Kwankwaso

“Kuma gobe (Litinin), Dattawan jihar Benuwe guda 35 za su ziyarci shugaban kasa a fadar Aso Rock dan ganawa da shi game da al’amarin.

“Akan ziyarar sa zuwa Benuwe, tabbas shugaban kasa zai ziyarci jihar Benuwe, da sauran wuraren da aka yi kashe-kashe kama jihar Ribas, Taraba da Kaduna," inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel