Matasa ga naku: Gwamati ta kamala shirin samar ma matasa miliyan 3 ayyukan yi

Matasa ga naku: Gwamati ta kamala shirin samar ma matasa miliyan 3 ayyukan yi

Akalla matasa miliyan uku ne zasu ci gajiyar wani tsarin rage zaman banza ta harkar noma, mai taken Livelihood Improvement Family Enterprise (LIFE), inji wata babban jami’ar gwamnati.

Uwargida Chinyere Ikechukwu Eneh, mataimakiyar darakta a ma’aikatan harkokin noma,ta bayyana haka ne a ranar Talata 16 ga watan Janairu yayin da ta kai ziyarar aiki jihar Enugu, inda tace jihohi 24 ne zasu fara amfana da tsarin a kasha na farko.

KU KARANTA: An yi wata takaddama a Fadar Shugaban kasa tsakanin EFCC da Abba Kyari

Daily Trust ta ruwaito jami’ar tana fadin matasa da shekarunsu sukafara daga 18- 40 zasu ci gajiyar wanann tsarin, wanda zai mayar da hankali wajen tabbatar samar da isashshen abinci ga Najeriya.

Matasa ga naku: Gwamati ta kamala shirin samar ma matasa miliyan 3 ayyukan yi

Matashi a gona

“Manufar wannan shiri shine samar dai isashshen abinci ga Najeriya, ciyar da tattalin arzikin kasa gaba da kuma samar ma matasa ayyukan yi. Yan Najeriya musamman matasa zasu amfana, zamu tabbatar da cewa rabinsu mata ne.” Inji ta.

A karkashin wannan tsarin za’a horas da matasa 1200 kan aikin noma,sa’annan za’a basu jari da kayan aiki na zamani, da kuma koya musu dabarun cinikayya. Matar tace za’a fara da kauyuka guda biyu a kananan hukumomi guda shidda na jihohi 24.

Daga karshe Uwrargida Ikechukwu ta shawarci jama’an jihar dasu dage, kuma su mayar da hankali wajen ganin sun ci moriyar wannan tsari, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

A nasa jawabin, babban sakataren ma’aikatan noma na jihar, Samuel Onyiaji ya yaba da wannan tsari, sa’annan ya bukaci a cigaba da wayar da jan jama’a kan tsarin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel