Bango ya tsage: rikita rikita ta kunno kai a tsakanin manyan muƙarraban shugaban kasa

Bango ya tsage: rikita rikita ta kunno kai a tsakanin manyan muƙarraban shugaban kasa

Rahotanni sun tabbatar da aukuwar wasu rikice rikice a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya kunshi manyan mukarrabansa, musamman Abba Kyari da Babagana Munguno.

Jaridar Premium Times ta ruwaito Abba Kyari, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da Babagana Munguno, mashawarcin shugaban kasa kan harkar tsaro suna gogoriyon nuna iko a tsakaninsu, wanda haka ka iya goga ma Buharin kan sa kashin kaza.

KU KARANTA: An yi wata takaddama a Fadar Shugaban kasa tsakanin EFCC da Abba Kyari

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faro ne a farkon watan Oktoban shekarar data shude, inda kamfanin man fetir ta kasa, NNPC ta sakaya wasu makudan kudade da suka kai naira biliyan 50.

Bango ya tsage: rikita rikita ta kunno kai a tsakanin manyan muƙarraban shugaban kasa

Buhari da Mungonu

Sai dai NNPC ta bayyana cewar Abba Kyari ne ya umarci NNPC ta boye kudaden, cewa kada a saka su a asusun bai daya,TSA, wannan ne ya sanya ofishin Munguno da ma EFCC suka shiga binciken wannan badakala, amma kwatsam sai shugaban hukumar tsaron ta sirri, DSS Lawal Daura ta shiga maganan ba tare da gayyata ba, inda ya jibge ma Kyari jami’an DSS don su kare shi daga kamen EFCC.

A wani faruwar kuwa, jami’an tsaron sun mamaye gidajen Abba Kyari da na Munguno dauke da muggan makamai, dayake makwabtan juna ne, hakan bai yi ma Munguno dadi ba, don haka ya turo Sojoji don su kwace makaman DSS, nan fa aka dan yi sa in sa, daga karshe dukkaninsu suka watse daga gidan.

Bango ya tsage: rikita rikita ta kunno kai a tsakanin manyan muƙarraban shugaban kasa

Buhari da Kyari

Bugu da kari, ana zargin Kyari yayi amfani da mukaminsa wajen sa hannu a nadin da shugaba Buhari yayi ma Abubakar Ahmed Rufai a matsayin sabon shugaban hukumar liken asiri, NIA, wanda hakan bai yi ma Munguno dadi ba a matsayin shi na mai bada shawara a kan lamurran tsaro, an yi hakan ba tare da saninsa ba, sai dai kawai yaji sanarwa a rediyo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel