Iyaye mata da matasa miliyan uku za su ci gajiyar shirin samar da ayyuka da gwamnatin tarayya za ta kaddamar

Iyaye mata da matasa miliyan uku za su ci gajiyar shirin samar da ayyuka da gwamnatin tarayya za ta kaddamar

- Gwamnatin tarayya zata kaddamar da shirin samar da ayyuka da ababen moriya rayuwa ga matasa da iyaye mata

- Matasa da iyaye mata miliyan uku ake sa ran za su karu da shirin samar da ayyuka da gwamnatin tarayya zata kaddamar

Iyaye mata da matasa miliyan uku za su ci gajiyar shirin samar da ayyuka ta hanyar noma da inganta rayuwar al’umma (LIFE) da gwamnatin taryya za ta kaddamar.

Wani babban jami’in gwamnatin tarayya ya bayyana haka a ranar Talata 16, ga Watan Janairu, 2018.

Mataimakiyar daraektan ma’aikatan harkan noma da raya karkara, Dakta Chinyere Ikechukwu-Eneh, ta ce jihar Enugu tare da jihohi 24 za su ci muriyar shirin (LIFE) da gwamantin tarraya zata kaddamar.

Iyaye mata da matasa miliyan uku za karu da shirin samar da ayyuka da gwamnatin tarayya za ta kaddamar

Iyaye mata da matasa miliyan uku za karu da shirin samar da ayyuka da gwamnatin tarayya za ta kaddamar

Dakta Chinyere Ikechukwu-Eneh, ta bayyana haka ne a lokacin da ta ziyarci, ma’aikatan kula da harkan noma da raya karkara na jihar Enugu.

KU KARANTA : ‘Yan sandan Kano sun bada belin kwamishinan da ya ce a jefi Kwankwaso

Chinyere ta ce iyaye mata da matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 40 za su karu da wannan shiri.

Ta ce manufar wannan shiri shine, tabbatar da abinci ya wadata a kasar, farfado tattalin arizki da samar wa dumbin matasa aikin yi ta hanyar noma.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel