Ka yi ƙarya kan kisan gillar da aka yiwa makiyaya a Taraba, CAN ta gaya wa Sanusi

Ka yi ƙarya kan kisan gillar da aka yiwa makiyaya a Taraba, CAN ta gaya wa Sanusi

Kungiyar kiristoci ta Najeriya wato CAN reshen jihar Taraba, ta ƙaryata iƙirarin sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, na cewar rayukan makiyaya sama da 800 sun salwanta a shekarar da ta gabata.

A yayin ganawa da 'yan jarida a makon da ya gabata, mai martaba sarkin Kano ya bayyana cewa, an kashe sama da makiyaya 800 a tsubirin Mambilla dake jihar Taraba a mako daya kadai.

A kalaman mai martaba, "Ni da kaina na mikawa gwamnatin tarayya sunaye tare da hotunan makiyaya 800 da aka yiwa yankan rago a jihar Taraba tare da sunayen wadanda suka aikata wannan ta'addanci amma babu wani mataki da aka dauka."

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Sai dai a wata sanarwa ta ranar talata a birnin Jalingo, shugaban kungiyar CAN na jihar, Rabaran Dakta Ben Ubeh ya ƙaryata ɓaɓatun sarki Sanusi, inda yake gargadinsa akan ya daina yadawa mutane ƙanzon kurege duba da cewar 'yan uwansa fulani ke faman kashe mutane a kowace rana a wasu sassan kasar.

KARANTA KUMA: Bamu amince a kirkiri burtali domin makiyaya ba a gonakin mu - Dattijan jihan Benuwe suka fadawa Buhari

Baya ga kiran gwamnatin tarayya akan ta watsalar da kudirin kirkirar burtalai, kungiyar ta kuma nemi gwamnatin akan tayi kaka gida dangane da halin da fiye da 'yan gudun hijira 10, 000 ke ciki a sanadiyar hare-haren makiyaya a jihar.

Kungiyar ta nemi daukacin al'ummar Najeriya akan su mike tsaye wajen yin Alla-wadai da kashe-kashen dake faruwa kamar yadda ta kuma buƙaci mutane su kasance masu lura da kuma yin addu'a ta gaske domin zaman lafiya a cikin ƙasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel