Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta yi Allah wadai da kisan Benue yayinda ta dawo daga hutu

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta yi Allah wadai da kisan Benue yayinda ta dawo daga hutu

- Majalisar dattawa ta yi Allah wadai da kisan Benue yayinda ta dawo daga hutu

- Shugaban majalisar dattawan, Bukola Saraki ya soki lamarin

- Saraki ya kuma gargadi ministoci, yan majalisa da sauran masu riko da mukaman gwamnati kan su ayiye 2019 a gefe su mayar da hankali ga shugabanci nagari a yanzu

Bayan dawowa daga hutu, a ranar Talata, 16 ga watan Janairu, majalisar dattawa ta yi Allah wadai da kisan Benue, cewa irin wannan zubda jinin baida gurbi a kasarmu.

Legit.ng ta tattaro cewa da yake sharhi akan kisan Benue shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, ya nuna takaici kan kashe-kashe da akayi a wasu yankunan kasar musamman wanda akayi kwanann nan a jihar Benue.

Saraki ya kuma gargadi ministoci, yan majalisa da sauran masu riko da mukaman gwamnati kan su ayiye 2019 a gefe su mayar da hankali ga shugabanci nagari a yanzu.

KU KARANTA KUMA: An gurfanar da tsohuwar ministar Abuja da wasu 2 a jihar Lagas (hotuna)

Ya ce abun kaico ne ga duk wani dan siyasa zai watsar da shugabanci mai kyau ya maida hankali kan siyasa.

Ya kuma yi magana kan karancin man fetur inda ya ce mutane ne ke haddasa shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel