Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasar Gambia, Adama Barrow

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasar Gambia, Adama Barrow

A yau Talata, 16 ga watan Junairu, shugaban Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasan Gambia, Adama Barrowa a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.

Shugabannin guda sun saka labule a yayin ziyaran.

Shugaba Adama Barrow dai karonsa na farko kenan zuwa Najeriya tun lokacin da aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasan Gambia ranan 19 ga Junairu, 2017.

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasar Gambia, Adama Barrow

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasar Gambia, Adama Barrow

Shugaba Buhiari zai shirya liyafa na musamman domin karrama wannan bako bayan tattaunawan diflomasiyya.

Shugaba Adama Barrow ya lashe zaben jihar Gambia ne inda ya lallasa tsohon shugaba Yahya Jammeh wanda a zabe.

KU KARANTA: An kasa cinma matsaya a zaman sulhu tsakanin makiyaya da manoma

Shugaba Buhari ya taka rawan gani a zaben yayinda Yahya Jammeh ya rantse ba zai bar karagar mulki ba duk da cewa an kada shi.

Shugaba Buhari ne ya jagoranci tawagar gamayyar tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma wato ECOWAS a rikicin zaben.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel