Sanatan da kotu ta dakatar da shi ya halarci taron zaman majalissar dattawa

Sanatan da kotu ta dakatar da shi ya halarci taron zaman majalissar dattawa

- Sanata Atai Aidoko Ali ya halarci zaman taron majalissar dattawa a ranar Talata duk da dakatar da shi da kotu daukaka kara ta yi

- Senata Atai ya Ali yace kotun daukaka kara bata dakatar dashi daga kan mukamin sa ba

Duk da umarnin kotun daukaka kara na dakatar da sanata mai wakiltar mazabar Kogi na tsakiya, Sanata Atai Aidoko Ali daga kan kujerar sa, sai da ya halarci zaman taron majalissar dattawa a ranar Talata a matsayin Sanata mai wakiltar mazabar sa.

Cif Wif ya sanar da majalissa dattawa cewa, Sanata Atai Aidoko Ali, ya na cikin su.

Kafin a sanar da majalissa ya halarci taron, sai da aka yi ganawar sirri da shi na sa’o’i biyu a cikin wani dakin taro.

Sanatan da kotu ta dakatar da shi ya halarci taron zaman majalissar dattawa

Sanatan da kotu ta dakatar da shi ya halarci taron zaman majalissar dattawa

Kotun daukaka kara dake zama a Abuja ta dakatar da Aidoko a matsayin sanata mai wakiltar mazabar Kogi na tsakiya, a ranar 18 ga watan Disamaba, 2018.

KU KARANTA : ‘Yan sandan Kano sun bada belin kwamishinan da ya ce a jefi Kwankwaso

Mista Aidoko ya karyata wannan hukunci da kotun zartar, inda yace babu inda kotu daukaka kara ta zartar da hukuncin dakatar da shi daga kan kujerar sa a zaman shariar da aka yi.

A wata takaradar shaida da jaridar PREMIUM TIMES Ta samu dagane da shariar, ta gano cewa sanata yayi karya, tabbas kotun daukaka kara ta dakatar da shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel