Haihuwar 'ya'ya rututu ta salwantar da wani auren shekaru 9 a jihar Legas

Haihuwar 'ya'ya rututu ta salwantar da wani auren shekaru 9 a jihar Legas

A ranar litinin din da ta gabata ne wata kotun jihar Legas ta salwantar da auren shekaru 9 dake tsakanin Mista Micahel Ayinde, da uwargidansa Glory Akinde, a sakamakon zubo masa da 'ya'ya rututu da take yi.

Alkalin kotun Mista Akin Akinniyi, ya ce babu wata makawa face salwantar da aure a sakamakon rashin amsa sammacin kotu da Glory tayi har aka kammala shari'ar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Mista Michael ya shigar da karar matarsa kotu ne a sakamakon haihuwar 'ya'ya rututu da take yi, inda yace cikin shekaru tara da aurensu ta zubo 'ya'ya har shida.

Haihuwar 'ya'ya rututu ta salwantar da wani auren shekaru 9 a jihar Legas

Haihuwar 'ya'ya rututu ta salwantar da wani auren shekaru 9 a jihar Legas

Mista Michael ya shaidawa kotun cewa, tun kafin aurensu sun yi da wajewa da uwargidansa na cewar 'ya'ya biyu kawai yake bukata wadanda zai iya dawainiya da su a sakamakon hali na rayuwa da yake hangawa.

KARANTA KUMA: Buhari ne zai sake nasara a zaben 2019 - Inji wani jigo na APC

A kalamansa yake cewa, "ya mai girma mai shari'a, mai daki na ta nufaci kashe ni da 'ya'ya. Tana haihuwar 'ya'ya rututu tamkar zomaye. Cikin shekaru tara da auren mu, ta haifi 'ya'ya har guda shida."

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel