An kasa cinma matsaya a zaman sulhu tsakanin makiyaya da manoma

An kasa cinma matsaya a zaman sulhu tsakanin makiyaya da manoma

- An gudanar da zaman sulhu tsakanin makiyaya da manoma a jihar Benuwe

- Anyi taron ne a gaban hukumar 'yan sanda

- Gwamna Ortom bai halarci taron ba

Hukumar 'yan sanda, karkashin babban Sifeton hukumar na kasa, Ibrahim Idris, ta jagoranci wani zaman sulhu tsakanin makiyaya da manoma a jihar Benuwe.

Ko a jiya saida dattijai da masu ruwa da tsaki a jihar Benuwe, karkashin jagorancin gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, suka ziyarci shugaba Buhari domin tattaunawa a kan batun rikicin makiyaya da manoma da ya dabaibaye jihar.

Saidai gwamna Ortom bai samu halartar zaman sulhun ba. Bamu samu wani rahoto da ya bayyana dalilin rashin halartar taron ba.

Rahotanni sun ce an kasa cinma matsaya yayin zaman sulhun.

An kasa cinma matsaya a zaman sulhu tsakanin makiyaya da manoma

An kasa cinma matsaya a zaman sulhu tsakanin makiyaya da manoma

Sakataren gwamnatin jihar Benuwe, Anthony Lor, ya bukaci da daga zaman sulhun tunda wadanda ya kamata su kasance a wurin basu samu damar halartar zaman ba.

KU KARANTA: Al'ummar garin Tunga sun tona asirin gwamna Ortom a gaban shugaban 'yan sanda bayan ya zarge su da mallakar bindigu

A jawabinsa, babban Sifeton 'yan sanda, Ibrahim Idris, ya roki dukkan bangarorin dake fafatawa a rikicin da su guji yin kalamai da kan iya hura wutar rikicin da aka fara shawo kansa.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Sanata Tilley-Gyado, ya ce babu bukatar yin sulhu tsakanin makiyaya da 'yan kabilar Tiv domin abokan wasa ne da suka dade suna zaune lafiya da juna. Kazalika Sanatan ya ce ya kamata shugaba Buhari ya sanar da su yadda dare daya rikici ya barke tsakanin abokan juna biyu.

Kazalika al'ummar makiyaya da manoma, yawancinsu 'yan kabilar Tiv, basu halarci zaman sulhun ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel