‘Yan sandan Kano sun bada belin kwamishinan da ya ce a jefi Kwankwaso

‘Yan sandan Kano sun bada belin kwamishinan da ya ce a jefi Kwankwaso

- Rundar 'yansandar jihar Kano sun gayyaci Alhaji Abdullahi Abbas ofishin su dangane da kalaman batanci da yayi akan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

- Abdullaji Abbas ya umarci magoya bayan gwamna Ganduje suyi wa Kwankwaso jifar shaidan idan ya shiga Kano

Rundunar ‘yansadar jihar Kano ta gayyaci kwamishinan ma'aikatar Ayyuka na musaaman, Alhaji Abdullahi Abbas, dangane da kalaman batanci da yayi akan tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

A cikin makon da ya gabata ne, Alhaji Abdullaji Abbas ya umarci magoya bayan gwamna Ganduje suyi wa Kwankwaso da magoya bayan sa jifar shaidan idan ya shiga Kano

A yanzu dai tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yana cigaba da shirye-shiryen shiga Kano tare da gangamin magoya bayan sa da ake sa ran za su haura sama da miliyan daya a ranar 31 Ga Janairu, 2018.

‘Yan sandan Kano sun bada belin kwamishinan da ya ce a jefi Kwankwaso

Abdullahi Abbas

Mai magana da yawun bakin rundunar yansandar jihar Kano, Magaji Majiya, ya fadawa manema labaru cewa sun gayyaci Abdullahi Abbas ne tare da wanda ya kai korafin MK Umar , kuma anyi musu tambayoyi dangane da kalaman da suka furta akan Kwankwaso.

KU KARANTA : Wani matashi ya lakadawa mahaifin sa dukan kawo-wuka

Magaji Majiya ya kara da cewa, an bada belin Abdullahi Abbas bayan an yi masa tambayoyi, “amma kuma karfin wannan kasassaba da ya yi, ta sa har yanzu ana ci gaba da bincike kan furucin nasa a ofishin hukumar binciken masu laifuka, wato CID".

Ya kara da cewa jami’an tsaro sun cafke wasu mutane dangane da wata ba hammata iska da aka yi tsakanin magoya bayan Ganduje da na Kwankwaso, a ranar Lahadin da ta gabata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel