Hukumar NDLEA ta kama masu fataucin miyagun kwayoyi 211 a jihar Kebbi

Hukumar NDLEA ta kama masu fataucin miyagun kwayoyi 211 a jihar Kebbi

- Hukumar NDLEA reshen jihar Kebbi ta kama masu fatauci da miyagun kwayoyi 211 da kuma kwayoyi da nauyin su ya kai kilogram 3,717.6 a shekarar bara

- Kididigan hukumar ya nuna cewa kwayar maganin Tramadol ne akafi fataucin sa a jihar

- Kwamandan hukumar ya mika godiya ga shugabanin al'umma da sarakunan gargajiya kan rawar ta suke takawa wajen fadakar da al'umma

Hukumar yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) reshen jihar Kebbi ta yi nasarar cafke mutane 211 da ake tuhuma da laifin fataucin miyagun kwayoyin kuma hukumar ta kwace miyagun kwayoyi wanda nauyin su ya kai kilogram 3,717.6 tsakanin watan Janairu zuwa Disambar 2017.

Kwamnadan hukumar na reshen jihar Kebbi, Suleiman Jadi ne ya bayar da wannan sanarwan a wata hira da yayi da manema labarai da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a birnin Kebbi.

Hukumar NDLEA ta kama masu safarar miyagun kwayoyi 211 a jihar Kebbi

Hukumar NDLEA ta kama masu safarar miyagun kwayoyi 211 a jihar Kebbi

DUBA WANNAN: Illolin shan kwayar maganin Paracetamol ba kan ka'ida ba - Masana

Jadi ya cigaba da cewa a shekarar da ta wuce, rundunar tayi nasarar aikewa da a kala mutane 20 zuwa gidan yari sannan akwai wasu shari'o'in da ke gaban babban kotun tarayya da ke Birnin Kebbi.

"A cikin shekarar da ta wuce, hukumar tayi nasarar kama kilogram 363.630 na ganyen wiwi, kilogram 3354.009 na abubuwan maye, kilogram 2387.039 na kwayar Tramadol da kuma kilogram 864.144 na maganin tari mai dauke da codeine.

"Hukumar ta lura cewa kwayar maganin Tramadol ne yafi yawa cikin kwayoyin da aka kama a shekarar bara," Inji shi

Jadi kuma ya mika godiyarsa ga masu sarautan gargajiya da shugabanin al'umma bisa kokarin da sukeyi wajen wayar da kan al'umma kan hatsarorin da ke tattare da amfani da miyagun kwayoyi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel