Yadda wani matashi mai shekaru 35 ya kwace jakunan kudi a harabar banki a Legas

Yadda wani matashi mai shekaru 35 ya kwace jakunan kudi a harabar banki a Legas

- Yadda wani matashi mai shekaru 35 ya kwace jakunan kudi a harabar banki na GTB a Legas

- Kotun Majistare ta Ikeja ta bukaci wanda ake tuhumar ya biya miliyan daya a matsayin kudin beli

- Alkalin kotun ya dakatar da shari'ar har zuwa Maris 23

Kotu ta ba da jinkirin belin wani matashi mai suna Festus Eboh, wanda ake zargin cewa ya kwace jakunan da ke dauke da N11.9 miliyan da dalar Amurka 30,000 a harabar wani banki a Legas.

Kotun Majistare ta Ikeja ta bukaci wanda ake tuhumar ya biya miliyan daya a matsayin kudin beli, da kuma shaidu guda biyu.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari , kotun ta ce dole ne daya daga cikin masu shaidun ya zama dan ’uwan wanda ake tuhuma, kuma ya kasance ma’aikaci tare da shaida na biyan haraji na shekara biyu ga gwamnatin jihar Legas.

Yadda wani matashi mai shekaru 35 ya kwace jakunan kudi a harabar banki a Legas

Hukuncin kotu

Dan sanda mai gabatar da kara, Benedict Aigbokhan ya shaida wa kotu cewa mutumin ya aikata wannan laifin ne a wani reshe na bankin GTB wanda ke Amuwo Odofin a Legas a karfe 12:30 na dare, ranar 14 ga Oktoba, 2017.

KU KARANTA: Matasan Daura 3,500 sun marawa Buhari baya karo na biyu

Jami’in ya yi zargin cewa wanda ake tuhuma da wasu wadanda ba’a san inda suke a halin yanzu ba sun yi yunkurin kwace jaka daga abokan ciniki da ke fitowa daga banki a wasu kwanaki daban-daban.

An dakatar da shari'ar har zuwa Maris 23.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel