Maina da EFCC: Babban kotu ta sake dage shari’an har sai watan Fabrairu

Maina da EFCC: Babban kotu ta sake dage shari’an har sai watan Fabrairu

- Wata babban kotun tarayya dake jihar Kaduna ta daga sauraron korafin da Abdulrasheed Maina ya shigar akan hukumar EFCC

- Lauyan hukumar EFCC shawara ya fada ma kotun cewa ba’a bi masu ta tsarin da ya dace ba sannan kuma suka bukaci sabon rana domin su shirya

- Bayan sauraron muhawaran, jagoran kotun, Saleh Shuaibu ya daga shari’an zuwa ranar Alhamis, 8 ga watan Fabrairu

Wata babban Kotu a jihar Kaduna ta sake daga karar da tsohon shugaban hukumar ayyukan fansho Abdulrasheed Mina ya gabatar, inda ya bukaci da tayi watsi da dokar hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) na 2004.

Maina a shekarar da ya gabata ne ya gabatar da kara a kotun inda yake bukatar kotun da ta bayyana dokar hukumar EFCC na 2004 a madadin izinin doka mara kan gado cewa dokar bata bi dokar majalisa ba kafin samun kafuwa a matsayin doka,don haka ne ya bukaci kotun da ta bayyana wannan dokar EFCC a matsayin rusashiya.

Amman a zaman da kotun tayi kan lamarin a ranar Litinin, lauya ga hukumar EFCC ya bayyanawa kotun cewa ba a aiko musu ba da asalin tsarin, sannan duk da haka ya bukaci sabuwar kwanan wata don bashi damar amfani da dukkan tsare-tsare da adireshi.

Maina ya tafi kotu ne bayan hukumar EFCC ta bayyana tana neman shi bisa zargin karkatar da kudaden fansho da aka karbo a lokacin da yake bauta a matsayin shugaban hukumar ayyukan fansho.

Maina da EFCC: Babban kotu ta sake dage shari’an har sai watan Fabrairu

Maina da EFCC: Babban kotu ta sake dage shari’an har sai watan Fabrairu

Daga cikin wadanda aka ambata a karar sun hada da- hukumar EFCC, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Shugaban Majalisan Dattawa Bukola Saraki da Shugaban Majalisan Wakilai, Yakubu Dogara.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kai hari Taraba, sun kashe wani basarake

Har ila yau ya bukaci kotun da ta hana duk wata hukumar tsaro daga kama shi bisa zargin rashawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel