Sai mun hada kai sannan Najeriya zata ci gaba - Atiku

Sai mun hada kai sannan Najeriya zata ci gaba - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa, lokaci yayi da ya kamata 'yan Najeriya su tashi tsaye wajen hada kai tare da kauracewa duk wani nau'in rabuwar kai a kasar nan, inda yace masu fafutikar son zukatansu ke gadar da matsala a Najeriya.

A ranar da ta gabata ne dattijon kasar ya bayyana hakan a yayin gabatar da batutuwansa domin bikin tunawa da ranar gwarazan dakarun sojin da suka riga mu gidan gaskiya wajen baiwa kasar nan tsaro.

Bayyana abubuwan da suka shafi aikin da sojojin kasar nan suka yi, Atiku ya kara da cewa akwai bukatar haɗin kai tsakanin 'yan Najeriya da sojoji wanda zai taimaka wajen samar da zaman lafiya, jituwa da girmamawa a kasar.

Atiku Abubakar

Atiku Abubakar

Atiku ya ci gaba da cewa, yana hararo wata sabuwar Najeriya da za tayi hannun riga da banbanton addinai da kuma kabilanci wadanda sune musabbabin matsalolin da kasar ke fuskanta a halin yanzu.

KARANTA KUMA: Kungiyar HURIWA ta gargadi Kwankwaso akan ziyarar jihar Kano

A kalamansa, "Fata na ga kasarmu shine ganin lokacin da maƙwabta na kabilu daban-daban da harsuna zasu ɗauki juna a matsayin ɗan'uwa da 'yar'uwa, lokacin da Kirista da Musulmai zasu koma ƙarƙashin igiyar Allah daya tilo wanda ya halicci dukkan mutane, lokacin da 'yan ƙasa zasu iya bayyana ra'ayoyin su da kuma matsalolin da ke cikin yankunansu, to kuwa a wannan lokaci ne kasar mu zata zauna lafiya."

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel