Kudin shiga tiriliyan N1.5 hukumar kwastam ke burin samu a shekarar nan

Kudin shiga tiriliyan N1.5 hukumar kwastam ke burin samu a shekarar nan

- Hukumar kwastam na burin samun tiriliyan N1.5 a matsayin kudin shiga a shekarar nan

- Jami'an hukumar 557 sun yi ritaya

- Hukumar ta yi karin girma ga wasu jami'an

Hukumar kwastam ta Najeriya ta bayyana cewar tana saka ran samun kudaden shiga tiriliyan N1.5 a shekarar nan.

Shugaban hukumar na kasa, Hameed Ali, ya sanar da haka yayin taron hukumar na farko a shekarar nan da aka gudanar a Abuja.

Kudin shiga tiriliyan N1.5 hukumar kwastam ke burin samu a shekarar nan

Hameed Ali

A jawabin da jami'in hulda da jama'a na hukumar, Joseph Attah, ya fitar a jiya Litinin, ya ce hukumar ta samu kudin shiga tiriliyan N1.37 a shekarar da ta gabata, adadin da ya wuce abinda hukumar ke saka ran samu, biliyan N770.57.

DUBA WANNA: Matasa miliyan daya zasu samu rancen kudi daga bilyan N10 da gwamati ta ware karkashin sabon shirin NEPRO

Hukumar ta ce kwanan nan za ta amince da karawa wasu jami'anta girma tare da tattauna yadda za'a kara wa jami'an hukumar albashi da biyansu wasu alawus-alawus.

Kazalika hukumar ta ace jami'anta 557 zasu yi ritaya a shekarar nan. Daga cikinsu akwai manyan mataimakan shugaban hukumar, mutum 11 masu taimakawa shugaban hukumar a jihohi da mataimakansu 27, da kuma karin wasu manyan jami'ai 23.

Anyi karin girma da canje-canjen wurin aiki ga wasu manyan Jami'an hukumar.

Shugaban hukumar ya bukaci jami'an da suka karin girma da su yi amfani da damar da suka samu domin bayar da gudunmawar su wajen kawo gyara da cigaban hukumar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel