Makiyaya sun kashe mutane fiye da Boko Haram - CAN

Makiyaya sun kashe mutane fiye da Boko Haram - CAN

- Rikcin makiyaya da manoma ya salwantar da rayuka da dama

- Makonda ya gabata, an hallaka akalla mutane 70 a jihar Benuwe

- Shugaba Buhari yayi alkawarin damke masu aikata irin wannan aika-aika

Kungiyar mabiya addinin Kirista a Najeriya ta yi ikirarin cewa hallaka rayukan da Makiyaya ke yi ya wuce na dukkan kungiyoyin da suka tayar da kayan baya a Najeriya.

Kungiyar, shiyar jihar Taraba ta yi wannan jawabi ne jiya inda ta zargi gwamnatin tarayya da jami'an tsaro da hadin baki wajen hallaka mutanensu.

Makiyaya sun kashe mutane fiye da Boko Haram - CAN

Makiyaya sun kashe mutane fiye da Boko Haram - CAN

Shugaban kungiyar na jihar Taraba yace: " Yanzu haka, shugaban kasa na goyon bayan yan kabilarsa dubi ga yadda yayiwa abin rikon sakeni kashi. Shugaban kasa ya san nayi da wuri."

A bara gwamnati ta alanta kungiyar yan faftukan neman Biafra wato IPOB da tsagerun Neja Delta a matsayin yan ta'adda amma ta gaza daukan irin wannan mataki a kan makiyaya wadanda sun fi kashe mutane ma fiye da Boko Haram.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel