Siyasa: An hana wani ministan Buhari daga ofishin gwamnati na tsawon shekaru 10

Siyasa: An hana wani ministan Buhari daga ofishin gwamnati na tsawon shekaru 10

- Gwamnatin Ekiti ta hana ministan ma’adinai daga mukamin ofishin gwamnati

- Majalisar zartarwa ta amince da wannan hukunci wanda ta kasance wani ɓangare na rahoton kwamitin bincike na shari'a

- Hadimin ministan ya ce a gudanar da bincike ne saboda neman farauta ko kuma ƙoƙarin cin mutuncin mai gidansa

Gwamnatin jihar Ekiti ta hana ministan ma’adinai kuma tsohon gwamnan jihar, Dokta Kayode Fayemi da tsohon kwamishinan kudi, Mista Dapo Kolawole daga rike mukamin ofishin gwamnati a jihar da Najeriya na tsawon shekaru 10.

Wannan ya biyo bayan amincewar majalisar zartarwa a kan rahoton da kwamitin bincike na shari'a ta bayar wanda gwamnatin jihar ta kafa domin gudanar da bincike kan gwamnatin Fayemi wanda ya kasance gwamna tsakanin 2010 zuwa 2014.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar cewa, wannan dakatarwa ya biyo bayan kin amincewar mutanen biyu su bayyana gaban kwamitin bincike ko da bayan da babbar kotun tarayya da ke Ekiti ta yanke hukuncin wanda ya kalubalanci kaddamar da kwamitin.

Siyasa: An hana wani ministan Buhari daga ofishin gwamnati na tsawon shekaru 10

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose

Rahoton ta ce, "Sun nuna rashin girmamawa ga ikon da aka kafa da kuma tafka almubazarranzi ayyukanin kwangilar da aka bayar a baya wanda ta sabawa bukatun jihar da ya kamata su kare. Saboda haka, an dakatar da su daga rike mukamin ofishin gwamnati a jihar Ekiti da kuma Najeriya baki daya”.

KU KARANTA: Ba wanda zai shiga rigar Buhari a zaben 2019 - Sakon PDP zuwa ga gwamnonin APC

Wata sanarwa da mataimakin na musamman kan harkokin yada labarai ga ministan, Mista Yinka Oyebode ya bayar, ya ce yayin da shugaban ya yi imanin cewa yana daga cikin nauyin gwamnatin jihar don duba kudade na jihar a kowane lokaci, amma ya kamata a yi hakan ba tare da nuna bambanci ko neman farauta da kuma ƙoƙarin cin mutuncin wani ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel