Kungiyar MURIC ta caccaki gwamnatin tarayya kan bayar da kyautar N40m ga tsofaffin shugabannin kasa

Kungiyar MURIC ta caccaki gwamnatin tarayya kan bayar da kyautar N40m ga tsofaffin shugabannin kasa

- Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta caccaki gwamnatin tarayya kan yunkurinta na biyan naira miliyan 40 ga ko wani tsohon shugaban kasa

- Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa zata biya naira miliyan 40 ga kowani tsohon shugaban kasa

- Kungiyar MURIC ta bayyana hakan a matsayin son kai da kuma karawa mai karfi karfi

Kungiyar kare hakkin Musulmi, MURIC, ta nuna rashin amincewa da biyan kudi naira miliyan 40 ga kowani tsohon shugaban kasa.

Kungiyar ta bayyana haka ne a wani jawabi da daraktanta, farfesa Ishaq Akintola ya gabatar, a Ibadan, a jiya Litinin, 15 ga watan Janairu.

A cewar Akintola, wannan rashin daidaituwa a tattalin arziki yana karfafa masu laifi, tunzura matasa, da kuma dakushe magoya bayan kasa da kawo jinkiri a yaki da rashawa.

Ya ce Gwamnatin Tarayya bazata iya yaki da rashawa ba ita kadai, amman ta bukaci mutane da su shiga yakin.

Kungiyar MURIC ta caccaki gwamnatin tarayya kan bayar da kautar N40m ga tsofaffin shugabannin kasa

Kungiyar MURIC ta caccaki gwamnatin tarayya kan bayar da kautar N40m ga tsofaffin shugabannin kasa

Ya bayyana cewa “Masu dimbin arziki” daga cikin tsoffin shuwagabannin kasa su dunga mikawa al’umma ba sai sun sha daga jininsu ba kuma, inda ya kara da cewa musulunci tana karfafa daidaituwar rabe-raben arziki.

KU KARANTA KUMA: Matasan Daura 3,500 sun marawa Buhari baya karo na biyu

Akintola ya daura laifi kan shawarar siyawa tsofaffin shuwagabanni motoci yayinda ba a sauraran koke koken masu amsan fansho.

Ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada yayi watsi da talakawan Najeriya ko kuma yarda da ci da ceto daga al’umma masu hadama da son zuciya, amman ya kasance mai mayar da hankali ga manufofinsa na kawar da kashe-kashen kudin Najeriya ba tare da amfani ba.

Ya bayyana cewa Allah zai tambayi kowani shugaba yanda ya gudanar da al’amuran mutanensa a ranar hisabi.

Kungiyar ta bayyana shawaran a matsaytin masu kin mutane, inda take korafi cewa tsarin Najeriya tana karawa “masu arziki arziki sannan talakawa talauci.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel