Buhari ne zabi na gari a shekarar 2019 - Shugaban kungiyar CACOL

Buhari ne zabi na gari a shekarar 2019 - Shugaban kungiyar CACOL

- Shugaban kungiyar CACOL, Debo Adeniran, ya ce Buhari ne zabi na gari a zaben shekarar 2019

- Ya yaba da kwazon shugaba Buhari

- Ya ce an samu canji mai ma'ana lokacin Buhari

Shugaban wata kungiya mai kyamar cin hanci da goyon bayan mulkin nagari (CACOL), Debo Adeniran, ya bayyana cewar shugaba Buhari ne kadai nagari duk ciki 'yan siyasar dake hankoron son mulkin Najeriya. Ya bayyana cewar matukar ba'a gudanar da taron yin garambawul ga kasa ba, dole 'yan Najeriya su cigaba da hakuri da juna.

Adeniran ya bayyana cewar shekarar 2017 da ta gabata ta zo da abubuwa da yawa da suka jawowa gwamnatin Buhari tafiyar hawainiya. Yana mai bayar da misali da rashin lafiyar da ya samu shugaba Buhari. Sannan ga dumbin matsalolin da yazo ya tarar a gwamnati.

Buhari ne zabi na gari a shekarar 2019 - Shugaban kungiyar CACOL

Shugaban kungiyar CACOL; Debo Adeniran

Saidai ya ce duk da matsalolin da shugaban ya tarar, ya yi namijin kokari kwarai da gaske wajen saita kasa a kan hanya madaidaiciya ta hanyar bunkasa noma da yaki da cin hanci, hanyoyin da ya ce sune kawai zasu kai Najeriya tudun mun tsira.

DUBA WANNAN: Nasarorin da Buhari ya samu ne suka jazawa mulkin jam'iyyar PDP na shekaru 16 bakinjini - Oyegun

Da yake magana a kan alkawuran da jam'iyyar APC ta dauka kafin hawa karagar mulki, Adeniran, ya ce duk da ba shine mai magana da yawun shugaban kasa ba, zai iya cewa kayar da jam'iyyar PDP shine abu mafi alheri da ya samu Najeriya.

Sannan ya kara da cewar "duk da cewar bani da masaniyar ko shugaba Buhari ya furta cewar zai kara yin takara, amma shine mafi cancanta daga cikin 'yan siyasar Najeriya dake hankoron son mulkar kasar. Ya fisu cancanta ta fuskar mutunci da kwatanta gaskiya."

Adeniran ya ce shawarar sa guda da zai bawa shugaba Buhari, ita ce, kada yakin neman zabe ya hana shi cigaba da gudanar da aiyukan gwamnati.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel