Buhari na da kyakkyawan tsari don kawo karshen rikicin makiyaya da manoma – In ji El-Rufai

Buhari na da kyakkyawan tsari don kawo karshen rikicin makiyaya da manoma – In ji El-Rufai

- Gwamnan Kaduna ya ce shugaba Buhari na da kyakkyawan tsari don kawo karshen rikici tsakanin makiyaya da manoma

- El-Rufai ya ce kai tsaye gwamnati ta dauki mataki don kawo karshen kashe-kashe a fadin kasar

- Gwamnan ya lura cewa, harakar tsaro wani kalubale ne da ke fuskantar kowace al'umma

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya bayyana a ranar Litinin,15 ga watan Janairu cewa gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Buhari tana da kyakkyawan tsari don kawo karshen rikici tsakanin makiyaya da manoma a kasar.

Legit.ng ta tattaro cewa, gwamna ya shaidawa manema labarai a wurin bikin ranar tunawa da ‘yan mazan jiya a Kaduna cewa kai tsaye gwamnati ta dauki mataki don kawo karshen rikicin.

"Mun sadu da ministan harkokin cikin gida, akwai shirye-shirye masu kyau don kawar da waɗannan batutuwa, ba na so in yi magana game da shirye-shiryen tsaro a rediyo da talabijin, amma ina so in tabbatar wa kowa, shugaban kasa da sauran jami'an tsaro suna iya kokarin su''.

Buhari yana da kyakkyawan tsari don kawo karshen rikicin makiyaya da manoma – In ji El-Rufai

Gwamna Nasir El-Rufai a bikin ranar tunawa da ‘yan mazan a Kaduna

Ya lura cewa, harakar tsaro wani kalubale ne da ba'a ta karewa a kowace al'umma, kuma sa hannu da sojoji suka yi ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar, ciki har da sassan jihar Kaduna.

KU KARANTA: El-Rufa'i ya bukaci korarrun malamai su sake neman aiki a jihar Kaduna

El-Rufa'i ya jaddada cewa, dala 1 biliyan daga asusun ‘Excess Crude Account’ da kungiyar gwamnoni ta tallafa wa gwamnatin tarayya cewa kungiyar ta yi ne don sayen kayan aiki wanda zai taimaka wa rundunar sojoji don kare al’ummar kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel