Matasan Daura 3,500 sun marawa Buhari baya karo na biyu

Matasan Daura 3,500 sun marawa Buhari baya karo na biyu

- Wassu matasa a karkashin kungiyar Daura Youth Vanguard daga yankin mazabar Sarkinyara A sun tsayar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Alhaji Aliyu Dahiru, wanda ya jagoranci kungiyar, ya karfafa bukatar sake tsayawa takarar shugaban kasar a zaben 2019

- Shugaban kungiyar ya lura cewa kiran ya zamo dole ganin yanda shugaban kasar ya fidda kasar daga kalubale da ta ke fuskanta

Akalla matasa 3,500 karkashin kungiyar Daura Youth Vanguard daga mazabar Sarkinyara A ward Polling Unit 003 a Daura ne suka hada kai don tsayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ta rahoto cewa anyi taron amincewa da hakan ne a mazabar shugaban kasa a garinsa a ranar Litinin.

Alhaji Aliyu Dahiru wanda ya jagoranci taron zuwa mazaban, ya karfafa bukata ga shugaban kasar da ya dubi bukatarsu ba tare da sharadi ba ya sake takara a zaben shugabancin kasa na 2019, inda yake karfafa cewa “Mun amince da yanda shugaban kasa yake jagorantar kasar nan.”

Mazabar Sarkinyara A polling Unit 3 ne mazabar da shugaban kasa Buhari yake kada kuri’arsa a dukkan zabuka.

Matasan Daura 3,500 sun marawa Buhari baya karo na biyu

Matasan Daura 3,500 sun marawa Buhari baya karo na biyu

Ya ce wassu al’amuran da suka ingiza kira ga shugaban kasar sun hada da canji da gwamnatin Buhari ta gabatar.

Dahiru ya ce kiran yazo a lokaci mafi cancanta musamman idan muka yi la’akari da yanda shugaban kasar ya fidda kasar daga halin kalubale da kuma sarrafa tattalin arziki zuwa harkar noma.

KU KARANTA KUMA: Za mu ambaci suna tare da kunyata yan siyasan Bayelsa dake daukar nauyin masu laifi

Ya lura cewa yaki da cin hanci da rashawa yana cigaba da samun nasara, kamar yanda aka samu natsuwa, riko da gaskiya da kuma nuna gasgiya a rayukan al’umma, inda yake mayar da hankali cewa Buhari ya kasance shugaba mai adalci.

Dahiru yayi sanarwa cewa kungiyan zata shirya haduwa a fadin yankunan kananan hukumomin Daura, Maiadua, Baure da Zango a watan fabreru.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel