Dandalin Kannywood: Kungiyar manyan jarumai sun yabawa Ganduje da ya yafewa Rahma Sadau

Dandalin Kannywood: Kungiyar manyan jarumai sun yabawa Ganduje da ya yafewa Rahma Sadau

Wata kungiyar manyan jaruman fina-finan Hausa dake da hedikwata a garin Kano watau Kano Actors’ Guild a turance ta bayyana jin dadin ta tare kuma da yabawa Gwamnan jihar kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje game da yafiyar da yayi wa jaruma Rahma Sadau.

Wannan dai yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da jaruman suka fitar ta bakin shugaban su Alhaji Alhassan Kwalle inda suka bayyana yafiyar a matsayin wani abu da yazo a cikin lokacin da ya dace.

Dandalin Kannywood: Kungiyar manyan jarumai sun yabawa Ganduje da ya yafewa Rahma Sadau

Dandalin Kannywood: Kungiyar manyan jarumai sun yabawa Ganduje da ya yafewa Rahma Sadau

Legit.ng ta samu a cikin sanarwar wadda Alhaji Rabi'u Rikadawa ya sanyawa hannu cewa suna da yakinin cewa su ba masu bata tarbiyya bane ba kuma suna bayar da gudummuwar su ga cigaban al'ummar jihar baki daya.

A wani labarin kuma, dandamalin farfajiyar masana'antar shirya-fina-finan Hausa ta cika da hotunan babbar diyar jarumi, furodusa, darakta kuma wani babban bango a masana'antar watau Fatima Ali Nuhu bayan da tayi bukin zagayowar ranar haihuwar ta.

Mun samu dai cewa diyar ta sa tayi bukin ne a ranar Asabar din da ta gabata inda kuma da yawa daga jarumai a masana'antar suka tayata murnar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel