Zamu kara zafafa yaki da cin hanci a wannan shekarar - Ibrahim Magu

Zamu kara zafafa yaki da cin hanci a wannan shekarar - Ibrahim Magu

- Ibrahim ya ce hukumar EFCC za ta kara kaimi wajen yaki da cin hanci a wannan shekarar

- Ya nemi hadin kan 'yan jarida

- Magu ya bayyana haka ne jiya a jihar Legas

Shugaban Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC), Ibrahim Magu, ya bayyana cewar zasu kara tsananta yaki da cin hanci a shekarar nan da muke ciki, tare da neman hadin kan kafafen watsa labarai.

Magu ya bayyana haka ne jiya a Legas yayin da ya kai ziyara ga alkalin alkalan jihar, mai shari'a Opeyemi Oke.

Zamu kara zafafa yaki da cin hanci a wannan shekarar - Ibrahim Magu

Ibrahim Magu

Ya kara da cewa "Kowa yana da rawar zai taka wajen dakile cin hanci. Ba abu ne ma sauki ba, amma da hadin kan jama'a zamu samu nasara. Wannan karon, zamu yaki cin da dukkan karfin mu, zamu tsananta matuka."

Kazalika, Magu, ya mika godiyar sa ga 'yan Najeriya bisa hadin kan da suke bawa hukumar EFCC, yana mai kara yin godiya ta musamman ga bangaren shari'ar bisa irin gudunmawar da ya ce suna ba shi.

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Kaduna za ta kashe N337.19m domin horar da malaman makarantu

"Ba zamu iya yaki da cin hanci mu kadai ba, muna bukatar hadin kan 'yan jaridu da bangaren shari'a. 'Yan jarida su guji karbar nagoro," inji Magu.

Masu nazarin yadda gwamnatin Buhari ke tafiyar da yaki da cin hanci sun jinjinawa kokarin gwamnati na yakar matsalar cin hanci a tsakanin 'yan siyasa da ma'aikatan gwamnati.

Tun kafin hawansa mulki, shugaba Buhari, ya taba furta cewar matukar Najeriya ba ta kashe cin hanci ba, cin hanci zai kashe Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel