Za mu ambaci suna tare da kunyata yan siyasan Bayelsa dake daukar nauyin masu laifi

Za mu ambaci suna tare da kunyata yan siyasan Bayelsa dake daukar nauyin masu laifi

Gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, ya jadadda kudirinsa na ambatan sunaye da kuma kunyata yan siyasan dake taimakawa masu aikata laifuka a jihar.

Kwamishinan bayanai da fuskantarwa, Daniel Iworiso-Markson, ya rahoto cewa Dickson ya yi wannan furuci ne a lokacin bikin ranar sojoji a Yenagoa a ranar Litinin, 15 ga watan Disamba.

Gwamnan wanda ya yaba ma hukumomin tsaro da gudunmawarsu wajen wanzar da zaman lafiya, tsaro da kuma ci gaban kasar ya yi korafin cewa wasu shugabannin siyasa ke haddasa rashin tsaro a jihar.

Dickson ya umurci shugabannin hukumomin tsaro daban-daban da su nuna jarumta da kwarewa wajen daukar matakin wanzar da tsaro kamar yadda kundin tsarin mulki ta tanadar.

Za mu ambaci suna tare da kunyata yan siyasan Bayelsa dake daukar nauyin masu laifi

Za mu ambaci suna tare da kunyata yan siyasan Bayelsa dake daukar nauyin masu laifi

Ya bayyana cewa hakki ne da ya rataya a wuyan jami’an sojoji da su gano da kuma kama masu laifi a ko wani sako da kusurwa na jihar.

A cewarsa, rashin daukar al’amarin tsaro da muhimmanci yana nuna tsoro da gazawar masu tsaro wanda bai kamata ya kasance haka ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An tsinci gawar dan majalisan jihar Taraba da akayi garkuwa da shi

Gwamnan ya kara da cewa duk garin da ya gaza shirya kan shi wajen bayyana masu laifi kamar irin masu garkuwa da mutane da sauransu, shine zai dauki alhakin ayyukan yan iskan garin.

Dickson ya kara da cewa a shirye yake da ya ba jami’an tsaro goyon baya domin suyi farautar duk wata kungiya ko mutumin da aka kama da wani aiki da zai zamo barazana ga zaman lafiya, ci gaba da kuma daidaituwar jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel