Hukumar NSCDC ta gano dabarun masu sayar wa Boko Haram man fetur

Hukumar NSCDC ta gano dabarun masu sayar wa Boko Haram man fetur

- Hukumar tsaro na NSCDC ta gano dabarar da wasu da ke sayar wa yan Boko Haram man fetir ke yi

- Hukumar tace sukan zuban fetir din ne a jarka kuma su nade cikin buhu sannan su ajiye a gefen titi, daga bayan yan ta'adan su kuma su dauka su ajiye kudi a nan

- Hukumar kuma ta sanar da cewa ta kama wani gagarumin mai damfarar al'umma mai suna Alh. Babakaka Baita wanda ya shahara wajen sayar da filayen bogi

Hukumar tsaro na NSCDC ta gano dabarun wadanda suke sayar wa yan ta'addan Boko Haram man fetur kuma ta datse kafar kasuwancin na su. A lokacin yake jawabi ga manema labarai a ranar Talata a Borno, Kwamandan hukumar, Abdullahi Ibrahim ya ce jami'an hukumar sun datse hanyoyin da yan ta'addan ke samun man fetir a hanyan Sambisa.

Hukumar NSCDC tayi raga-raga da masu sayar wa yan Boko Haram man fetur

Hukumar NSCDC tayi raga-raga da masu sayar wa yan Boko Haram man fetur

Ya cigaba da cewa sun gano dabarar da masu sayar da man sukeyi kuma sun dauki mataki a kai. Ibrahim yace dabarar da masu sayar da man sukeyi shine zuba fetir din cikin galan sannan sai su nade cikin buhu su ajiye gefen titi, daga bayan yan ta'adan su kuma za su dauki man fetir din su ajiye kudi a nan.

DUBA WANNAN: Hukumar NDLEA ta kama masu fataucin miyagun kwayoyi 211 a jihar Kebbi

Ibarhim ya yi juyayin yadda rundunar ba ta kama masu sayar daman ba domin sun tsere sun bar man fetir din lokacin da suka hango motar rundunar, sai dai ya nuna ma manema labarai wasu daga cikin jarkokin man fetir din da rundunar ta kwace.

Rundunar kuma ta nuna wa yan jarida wani gagarumin dan damfara wanda ya shara wajen yiwa mutane zamba wajen siyar da filaye, Alhaji Babakaka Baitu ya bayyana cewa ya damfari al'umma kudin da ya kai miliyan 20.

Rundunar ta dade tana neman sa amma sai yanzu tayi nasarar kama shi domin baya zama wuri daya, yawo yakeyi a garuruwan Maiduguri. Ibrahim yace tun bayan kama Baitu, rahotannin damfarar fili ya ragu a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel