Siyasar Kano: Ganduje ya kara gamuwa da wani babban cikas

Siyasar Kano: Ganduje ya kara gamuwa da wani babban cikas

Dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano a shekarun 2011 da kuma 2015 din da suka gabata watau Malam Salihu Sagir Takai ya kaddamar da wani kwamiti mai mutane biyar game da kudurin takarar ta sa a zaben 2019 mai zuwa.

Wannan kwamitin dai kamar yadda muka samu labari an kafa shi ne da zummar lalubo hanyoyi mafi sauki da dan takarar zai iya bi ya lashe zaben mai zuwa tare kuma da kula da sauran kungiyoyin dan takarar da za su fito.

Siyasar Kano: Ganduje ya kara gamuwa da wani babban cikas
Siyasar Kano: Ganduje ya kara gamuwa da wani babban cikas

Legit.ng ta samu cewa kadan daga cikin mambobin kwamitin dai sun hada ne da Alhaji Ali Datti Yako, Hon. Ubale Jakada Kiru, Dr. Mahmoud Baffa Yola, Dr. Bashir Shehu Galadanchi, Barrister Faruk Iya Sambo, Hon. Garba Shehu Fammar da kuma Hon. Idris Garba Unguwar Rimi.

Sauran sun hada da Hajiya Aishatu Mai-Jama’a, Comrade Munnir Matawalle, Hon. Sanusi Sani Barkum, Alhaji Lawal Tudunwada, Alhaji Tijjani Labaran Dambatta, Alhaji Kabiru Muhammad Tarauni, da Alhaji Muktar Darki wanda zai zama Sakataren kwamitin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng