El-Rufa'i ya bukaci korarrun malamai su sake neman aiki a jihar Kaduna

El-Rufa'i ya bukaci korarrun malamai su sake neman aiki a jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta baiwa korarrun malamai 21, 000 da basu yi nasarar tantancewa ba wata sabuwar dama na sake yin la'akari a garesu, inda tace suna iya sake neman aiki a yayin da take yunkurin dibar ma'aikata a jihar.

Kimanin korarrun malamai 12, 000 ne suka nuna bukatarsu ta neman aiki yayin da sauran suka kasance ba su aikata hakan ba.

Mallam Nasir El-Rufa'i

Mallam Nasir El-Rufa'i

A yayin da yake amsa tambayoyi a lokacin ganawa da shugabannin kananan hukumomi da sakatarorinsu na ilimi a jihar Kaduna, gwamna Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa zai sake baiwa korarrun malamai damar ta daukansu aiki a yayin da ma'aikatar ilimi ke yunkurin daukar ma'aikata.

KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An tsinci gawar dan majalisan jihar Taraba da akayi garkuwa da shi

Mallam El-Rufa'i yake cewa, ba mu da sha'awar ture kowa, sai dai manufar itace tankade tare da rairaye nagartattun malamai a ma'aikatar ilimi ta jihar. Dalilin haka ya sanya zamu maye gurbin korarrun malamai 21,780 da sabbi guda 25, 000.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel