An kashe wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane da wasu 4

An kashe wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane da wasu 4

- An kashe babban dan fashi da garkuwa da mutane, Akpafit

- Wannan dan fashi ya addabi jama'an Ukanafum a jihar Akwa Ibom

Gamayyar jami'an yan sanda, DSS da soji sun hallaka kasurgumin mai garkuwa da mutane, Iso Akpafit.

Rahotanni sun nuna cewa Akpafit dan ta'adda ne wanda addabi al'ummar karamar hukumar Ukanafun da ke jihar Akwa Ibom.

Kana ana zarginsa da kashe-kashen jama'a, rikicin yan daba, fashi da makami da kuma garkuwa da mutane a yankin.

An samu labarin cewa Akpafit na cikin mutane da hukuma ke nema ruwa a jallo kafin dubunsa ya cika a jiya Litinin.

An kashe wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane da wasu 4

An kashe wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane da wasu 4

Wani mazaunin garin, Mr. Edet Akpan, wanda ya tabbatar da faruwa ya ce lallai ya ga gawar Akpafit yayinda aka tafi da shi.

KU KARANTA: EFCC tayi nasara kan Patience Jonathan a Kotu

“Yanzu da nike muku magana mutane na cikin farin ciki da shewa a Ukanafum. Ni kaina na ji dadi n shaida wannan abu.

Duk da cewa an kashe wasu abokansa 4, jama'an mu sun fi farin cikin kisan shugaban, Akpafit. An fada mana cewa an kaima bokan su kuma an harbe shi a kafa, bamu san halin da yake ciki ba"

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a:

https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a

http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel