Osinbajo zai gabatar da takarda game da Gwamnatin Buhari a babbar Jami’ar Duniya

Osinbajo zai gabatar da takarda game da Gwamnatin Buhari a babbar Jami’ar Duniya

- Farfesa Osinbajo zai gabatar da takarda a Jami’ar Harvard ta Amurka

- Duniya ta yabawa irin kokarin da Gwamnatin Kasar tayi a harkar tattali

- Kwamitin Osinbajo ta yi aiki wajen saukake harkar kasuwanci a Najeriya

Mun samu labari cewa Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bar Najeriya zuwa Kasar domin wani taro a Jami’ar kasar. Ana sa rai Farfesa Osinbajo zai dawo gida a gobe Laraba.

Osinbajo zai gabatar da takarda game da Gwamnatin Buhari a babbar Jami’ar Duniya

Mataimakin Shugaban kasa ya tafi Amurka zai yi lacca a Harvard

Farfesa Osinbajo zai yi jawabi ne a Jami’ar Harvard ta Kasar Amurka game da tsare-tsare da manufofin Gwamnatin Shugaba Buhari musamman a sha’anin saukake kasuwanci a kasar inda Mataimakin Shugaban kasar yayi namijin kokari.

KU KARANTA: Zan yi takarar Shugaban kasa a zaben 2019 – Donald Duke

Wannan ne karo na farko a Tarihi da Jami’ar za ta dauki wani kwas na musamman game da Afrika saboda irin kokarin da Gwamnatin Shugaba Buhari tayi na bada damar kasuwanci da habaka tattalin arzikin Kasar inji Fadar Shugaban kasar.

Mataimakin Shugaban kasar ya saba magana kan irin masu basirar da ake da su a fannoni da dama a Afrika. Osinbajo ya bar Najeriya ne a jiya inda zai gabatar da jawabin na sa a yau. Kuma zuwa gobe da yamma ake sa ran dawowar sa gida.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel