Buhari ne zai sake nasara a zaben 2019 - Inji wani jigo na APC

Buhari ne zai sake nasara a zaben 2019 - Inji wani jigo na APC

Wani jigo na jam'iyyar APC a jihar Abia, Prince Chamberlain Adiaso, ya bayyana cewa tabbas shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tsaya takara kuma shi zai sake lashe zaben 2019 mai gabatowa.

Prince Adiaso ya bayyana hakan a yayin ganawa da 'yan jarida a birnin Abuja, inda yace a ranar 8 ga watan Maris 'yan Najeriya zasu gudanar da tattaki a birnin Landan domin bayyanawa duniya irin girman soyayyarsu ga shugaba Buhari.

Shugaba Buhari

Shugaba Buhari

Wannan batu na jigon jam'iyyar APC yazo a sakamakon jadawalin gudanar da zabe da hukumar INEC ta fitar a makonnin da suka gabata, inda ya bayyana kudirinsa na tsayawa takara da kuma lashe kujerar gwamnan jihar Abia.

KARANTA KUMA: Rushe Rumfuna: Gwamna Obiano ya fusata masu sana'ar karuwanci a jihar Anambra

A kalamansa, "a gani na ido lafiyar shugaba Buhari tamkar ta matashi ce da ya karbi takardarsa ta tafiya bautar kasa."

Yake cewa, cikin yarda ta Ubangiji shugaba Buhari zai sake tsayawa takara kuma ya lashe kujerar fadar shugaban kasa domin kuwa ya samu lafiya da karsashin mulki a halin yanzu.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel