Zan yi takarar Shugaban kasa a zaben 2019 – Donald Duke

Zan yi takarar Shugaban kasa a zaben 2019 – Donald Duke

- Tsohon Gwamnan Najeriya ya dauki damar zama Shugaban kasa a 2019

- Mista Donald Duke yace yana da duk abin da ake nema na mulkin Kasar

- Ya kuma yi kira musamman ga Matasa da su shirya fita zaben da za ayi

Mun samu labari cewa daga Jaridar Vanguard tsohon Gwamnan Jihar Kuros-Riba watau Donald Duke ya bayyana niyyar sa na tsayawa takarar Shugaban kasar Najeriya a zabe mai zuwa na 2019.

Zan yi takarar Shugaban kasa a zaben 2019 – Donald Duke

Tsohon Gwamnan Kuros Riba tare da Shugaban kasa Buhari

Donald Duke ya tabattar da wannan ne a wajen wani taron lacca da aka yi game da Najeriya a babban Birnin Tarayya Abuja. Tsohon Gwamnan kasar yace yana da damar tsayawa takarar kujerar Shugaban kasa a Najeriya.

KU KARANTA: Tazarcen Shugaba Buhari zai cabawa wasu lissafi

Mista Duke yace zai fara shirin da ya dace inda yake ganin ya isa ya mulki kasar. Donald Duke ya kuma yi kira ga Matasan Kasar da su dage wajen shiryawa zabe domin ganin an zabi wanda zai kai kasar nan ga ci a halin yanzu.

Tsohon Gwamnan ya nemi matasa ka da su karaya tun da har su ka zo Duniya. A cewar Donald Duke, duk su Sardauna sun yi mulki ne su na masu shekaru 20 da ‘yan kai. Ya kara da cewa dole a sa Matasa a gaba a horar da su don gobe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel