An yi wata takaddama a Fadar Shugaban kasa tsakanin EFCC da Abba Kyari

An yi wata takaddama a Fadar Shugaban kasa tsakanin EFCC da Abba Kyari

- Shugaban EFCC Magu ya nemi ya damke Malam Abba Kyari

- Hakan ya jawo rikici tsakanin Jami'an tsaro na kasar da EFCC

- EFCC na zargin Abba Kyari da aikata ba daidai ba a kujerar sa

Mun samu labari cewa Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu yayi kokarin kama Shugaban Ma'aikatan da ke Fadar Shugaban kasa watau Abba Kyari amma hakan bai yiwu ba.

An yi wata takaddama a Fadar Shugaban kasa tsakanin EFCC da Abba Kyari

Shugaban EFCC Magu na neman debo ruwan dafa kan sa
Source: Facebook

Jaridar nan ta Sahara Reporters ce dai ta kawo wannan labari inda tace yi an wata takaddama a Fadar Shugaban kasar tsakanin Jami'an na EFCC bisa umarnin Shugaban Hukumar Ibrahim Magu da kuma Malam Abba Kyari.

KU KARANTA: EFCC tayi nasara kan Patience Jonathan a Kotu

An yi wata takaddama a Fadar Shugaban kasa tsakanin EFCC da Abba Kyari

An nemi a kama Abba Kyari a cikin Fadar Shubaban kasa

Shugaban Hukumar DSS Lawal Daura ne ya sanar da Kyari abin da ne faruwa don haka yayi amfani da Jami'an sa wajen kokarin hana a damke Shugaban Ma'aikatan na Aso Villa. Sai dai ba a ba ma'aikatan na DSS shiga Fadar ba.

Ibrahim Magu hana Legas lokacin da duk wannan abu ya faru. Majiyar mu tace bayan nan ne Shugaba Buhari ya nemi ganawa da Ibrahim Magu. Wasu na cewa hakan dai ya fusata Shugaban kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel