Kotu ta kara yin na'am da a karbe wasu makudan Biliyoyi daga hannun Patience Jonathan

Kotu ta kara yin na'am da a karbe wasu makudan Biliyoyi daga hannun Patience Jonathan

- Kotu ta nemi a karbe wasu kudi daga hannun Matar Jonathan

- Matar tsohon Shugaban kasar ta daukaka kara a Kotun Kasar

- Sai dai Kotun daukak karar tace a cigaba rike kudin Uwargidar

Mun samu labari cewa Lauyan da ke kare Tsohuwar Uwargidar Najeriya Patience Jonathan watau Mike Ozekhome ya sha kashi a Kotun daukaka kara inda aka tabbatar da hukuncin da babban Kotun Tarayya da ke Legas ta dauka.

Kotu ta kara yin na'am da a karbe wasu makudan Biliyoyi daga hannun Patience Jonathan

Patience Jonathan ta sha kashi a Kotun daukaka kara

A karshen makon can ne Hukumar EFCC ta kara samun nasara a kan Matar tsohon Shugaban kasar a Kotu inda aka nemi lallai a rike wasu kudi na tsohuwar Uwargidar kasar saboda zargin cewa ba ta hanyar kwarai ta samu kudin ba.

KU KARANTA: Magu zai karbe kudin Matar tsohon Shugaban kasa

Kamar yadda EFCC ta roka, a baya dama Alkali CMA Olatoregun ya nemi a karbe wasu kudi har kusan Dala Miliyan 6 da kuma wasu sama da Naira Biliyan 2 da rabi da ke asusun matar tsohon Shugaban kasar Dr. Goodluck Jonathan.

Lauyoyin da ke kare Madam Jonathan ba su amince da wannan hukunci ba. Sai dai Kotun daukaka kara na kasar tace abin da babban Kotun tayi yayi daidai inda Alkaki Mojeed Owoade yace kar a maidawa Mai dakin Jonathan kudin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel