Sabuwa: Mutane 3 sun mutu sanadiyar cutan zazzabin Lassa

Sabuwa: Mutane 3 sun mutu sanadiyar cutan zazzabin Lassa

- Zazzabin Lassa ya dawo kuma

- Akalla mutane 3 sun hallaka zuwa yanzu

A yau Litinin, 15 ga watan Junairu Gwamnatin jihar Ebonyi ta tabbatar da mutuwan likita da ma'aikicar asibiti sanadiyar cutan Lassa.

Kwamishanan lafiyan jihar, Daniel Umezuruike, ya bayyana wannan ne a garin Abakaliki, babban birnin jihar.

Ya ce wani maras lafiya da daya daga cikin likitocin ya samu lafiya. Mara lafiyan shine na farko da aka samu da rashin lafiyan.

KU KARANTA: Kuma dai! Mutane 5 sun hallaka a sabuwar gobara a jihar Legas

“A makon da ya gabata, an samu masu cutan amma jiya na samu labarin cewa wani likita ya mutu sanadiyar cutar Lassa. Munyi gwajin kala 12 kuma mun tabbatar da hakan."

Kwamishanan ya ce wadanda abin ya shafa su kawo kansu asibiti bayan su gaji da shan magungunan sa kai.

“Daya daga cikinsu na kula da kanshi. Sai ya tafi asibitin Mater a Afikpo. Daga baya likitoci 2 suka bashi shawara yaje asibitin gwamnatin tarayya da ke Abakalili."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel