Kuma dai! Mutane 5 sun hallaka a sabuwar gobara a jihar Legas

Kuma dai! Mutane 5 sun hallaka a sabuwar gobara a jihar Legas

- Akalla mutane 2 sun rasa rayukansu a gobara da safe a unguwar Magodo

- Da rana kuma aka sake wani gobara a unguwar Badagry dukka sanadiyar iskar Gas

Akalla mutane 5 sun rigamu gidan gaskiya kuma wasu 5 sun jikkata a sabuwar gobarar iskar gas da ya faru a Ajara Vevho, unguwar Badagry, jihar Legas.

Gobaran ya faru ne a wani shago yayinda masu shagon ke kokarin shigar da Silinda cikin shago.

Kuma dai! Mutane 5 sun hallaka a sabuwar gobara a jihar Legas

Kuma dai! Mutane 5 sun hallaka a sabuwar gobara a jihar Legas

Wani rahoto ya nuna cewa wayan tarho ne ya sabbaba wannan mumunan gobara amma ba'a tabbatar da hakan ba.

KU KARANTA: An tsinci gawar dan majalisan jihar Taraba da akayi garkuwa da shi

Dikraktan hukumar kawar da gobara a jihar Legas, Rassak Fadipe, ya tabbatar da wannan rahoto ga jaridar Tribune kuma ma'aikatansa na iyakan kokarinsu wajen kashe gobaran.

Wadanda suka rasa rayukansu ya kunshi wasu yan shagon gyaran gashin da kuma dan achaban da ke tsaye a gaban shagon.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel