Bai kamata Gwamnoni su fara kiran tazarcen Shugaba Buhari ba – Timi Frank

Bai kamata Gwamnoni su fara kiran tazarcen Shugaba Buhari ba – Timi Frank

- Wani babba a Jam’iyyar APC ya soki su Gwamna Nasir El-Rufai

- Timi Frank yace bai dace a fara kawowa Buhari batun tazarce ba

- Kwamared Frank yace mutane da dama na wahala a mulkin nan

Mun samun labari daga Jaridar Daily Trust ta Kasar nan cewa wani babba a Jam’iyyar ‘Dan APC mai mulki yayi kaca-kaca da Gwamnonin Jam’iyyar na Arewa da su ka nemi Shugaba Buhari ya sake neman takara a zabe mai zuwa na 2019.

Bai kamata Gwamnoni su fara kiran tazarcen Shugaba Buhari ba – Timi Frank

Da dama na wahala a cikin Najeriya inji Frank

Mataimakin mai magana da yawun Jam’iyyar APC a da Mista Timi Frank yayi tir da Gwamnonin Jam’iyyar da su ka ziyarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a wancan makon inda su kayi kira Shugaban ya nemi ya zarce a zabe mai zuwa.

KU KARANTA: Buhari ba zai ceci Gwamnonin APC ba - PDP

Kwamared Timi Frank ya fitar da wani jawabi a Birnin Tarayya Abuja jiyan nan inda yace wannan abu da Gwamnoni su kayi ya nuna rashin imani da tausayin halin da mutanen Najeriya ke ciki a wannan lokaci a Gwamnatin Shugaba Buhari.

Frank ya shawarci Gwamnonin Jam’iyyar da su nemi Shugaban kasa Buhari ya kawo tsarin da za a tallafawa mutanen da su ke cikin kunci a Najeriya a maimakon wannan yunkuri na su na son kai da su ke kokarin saidawa Shugaban kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel