Yanzu Yanzu: An tsinci gawar dan majalisan jihar Taraba da akayi garkuwa da shi

Yanzu Yanzu: An tsinci gawar dan majalisan jihar Taraba da akayi garkuwa da shi

- Hosea Ibi dake wakiltan Takum I a majalisar dokokin jihar Taraba ya mutu

- An sace dan majalisan ne a ranar Asabar 30 ga watan Disamba, 2017 a garinsa

An tsinci gawar Hosea Ibi dan majalisan dake wakiltan Takum I na majalisar dokokin jihar Taraba, a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu, bayan an sace shi a ranar a 2017, jaridar Vanguward ta ruwaito.

Wasu yan bindiga ne suka sace dan majalisan a ranar Asabar, 30 ga watan Disamba, 2017, a mahaifarsa na Takum.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wadanda suka yi garkuwa da dan majalisar dake wakiltan Takum a majalisar dokokin jihar Taraba Hosea Ibi, sun bukaci a basu naira miliyan 75 sannan su sake shi.

KU KARANTA KUMA: Bamu amince a kirkiri burtali domin makiyaya ba a gonakin mu - Dattijan jihan Benuwe suka fadawa Buhari

Wani majiya daga yan uwansa da ya nemi a sakaye sunansa ya fada ma jaridar The Punch, a ranar Alhamis, 4 ga watan Janairu cewa masu garkuwan sun kira makusancin mamacin wanda ya kasance dan majalisar dokokin jihar, inda suka bukaci kudin fansar da zasu karba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel