Albashin malamai: Ku ci gaba da zama a gidajen ku har zai an biya ku – In ji NUT

Albashin malamai: Ku ci gaba da zama a gidajen ku har zai an biya ku – In ji NUT

- NUT ta bukaci mambobinta su ci gaba da zama a gida har zai an biya su albashi

- Jihohi goma ne ake sa ran sun kasa biyan albashi na malamai makarantu

- Babban sakataren kungiyar ya ce duk da rokon da NUT ta yi wa gwamnonin a shekara ta 2017, amma har yanzu wasu sun kasa biya

Kungiyar malamai na Najeriya (NUT) ta bukaci malamai a jihohi 10 da suka kasa biyan albashi cewa su ci gaba da zaman gida har sai an biya dukkan kudin albashin su.

Dokta Mike Ike-Ene, babban sakataren kungiyar, ya yi wannan magana kan wani umarni a wata hira da manema labarai a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu a birnin Abuja.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari , Ike-Ene ya bayyana cewa goma daga cikin jihohi 36, har yanzu malamai suna bin albashi na watanni, duk da kudin Paris Club da jihohin suka samu daga shugaba Muhammadu Buhari.

Albashin malamai: Ku kasance a gidajen ku har zai an biya ku – In ji NUT

Wani malami

Ya ce jihohin sun hada da; Abiya, Adamawa, Bayelsa, Binuwai, Delta, Ekiti, Kogi, Ondo, Kwara da Taraba.

KU KARANTA: Ana shirin kammala Jami’ar fasaha ta Abuja AUTA

Ike-Ene ya bayyana cewa, ƙungiyar ta umurci membobinta a jihohin da wannan lamarin ta shafa, musamman malamai na makarantar firamare cewa kada su koma aiki har sai an biya su.

Ya kuma ce duk da rokon da NUT ta yi a shekara ta 2017 ga gwamnonin cewa su yi amfani da lokacin bukukuwan Kirsimeti don biya wadannan kudaden, amma har yanzu wasu sun kasa yin haka.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel