Har yanzu akwai makiyaya a yankunan mu – In ji wasu mazaunan Binuwai

Har yanzu akwai makiyaya a yankunan mu – In ji wasu mazaunan Binuwai

- Wasu mazaunan Binuwai sun koka cewa har yanzu akwai makiyaya a yankunan su

- Mazaunan sun koka cewa ba za mu iya koma gida haka nan kawai ba tare da isashen tsaro ba

- Jami’an hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar Binuwai ya ce an samar da isasshen tsaro a wuraren da rikicin ta shafa

Ko da yake makonni biyu ke nan tun da lamarin ya faru, ammam wasu mazaunan yankin sun bayyana cewa dukkannin kananan hukumomin biyu da makiyaya wadanda ake tuhuma da aikata wannan mumunan hare-hare suna ci gaba da kasancewa a yankunan.

"Makiyaya har yanzu suna yankunan mu, kuma ba za mu iya koma gida haka nan kawai ba", in ji Fafa, daya daga cikin manoma ‘yan gudun hijirar da suka bar gidajensu daga kauyen Guma ya shida wa jaridar TheCable.

Fafa da iyalinsa sun gudu don kare rayukansu lokacin da suka ji labarin hare-hare a kauyen da ke kusa.

Har yanzu akwai makiyaya a yankunan mu – In ji wasu mazaunan Binuwai

Rikicin Binuwai

Ya ce, "Yanzu dai mun gudu, amma muna fatan jami'an tsaro zasu so su taimaka mana don mu koma gida saboda mun san cewa wadannan makiyayan za su kwashe dukiyarmu, amma babu wanda ke wurin don samar da tsaro a gare mu", inji shi.

KU KARANTA: Har yanzu bamu samu wani ingantaccen shugabanci a Najeriya ba – Fafesa Ango Abdullahi

A makarantar firamare a Daudu, wani kauye a Guma inda Fafa da daruruwan 'yan gudun hijirar ke zaune, mutane suna matukar damuwa game da yanayin tsaro a yankin.

Elisha, wani manomi da shi ma ya yi hijira, ya shaida wa majiyar Legit.ng cewa ‘yan sanda ma sun gudu yayin da suka gani wasu daga cikin makiyayan.

Lokacin da aka tuntube jami’an hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar Binuwai, Musa Yamu, ya tabbatar cewa hukumar ta samar da isasshen tsaro a wuraren da lamarin ta shafa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel