Ana shirin kammala Jami’ar fasaha ta Abuja AUTA

Ana shirin kammala Jami’ar fasaha ta Abuja AUTA

- Ana daf da kammala wata Jami’ar fasaha a Birnin Tarayya

- An yi sama da shekaru 10 ana ginin wannan Jami’a a Abuja

- Za a maida kwalejin ilmin da ke Zuba zuwa wani sabon sashe

Mun samu labari cewa kwanan nan ake shirin kammala ginin Jami’ar fasahar da ake ginawa a babban Birnin Tarayya Abuja. Kuma ba da dadewa ba za a fara shirin bude Makarantar a fara karatu a banan nan.

Sakataren harkar ilmi na Birnin Tarayya Abuja Isa Maina ya zanta da ‘Yan Jaridar Daily Trust a cikin wannan watan inda ya bayyana masu abin da ya hana bude Jami’ar nan ta fasaha da ake ginawa a Garin na Abuja.

KU KARANTA: Wani 'Dan Majalisa ya nemi a marawa Shugaba Buhari baya

Malam Isa Maina yace sama da shekaru 10 kenan ana kokari a kammala aikin Jami’ar ta AUTA ta Abuja amma abin bai yiwu ba. Ana dai sa rai a shekarar banan nan ne za a karasa aikin kuma a fara karatu a makarantar.

Sakataren yace Gwamnati tayi sakaci wajen saka mutanen da ba su san aiki a harkar Jami’ar ba. Bayan haka Sakataren ya kuma bayyana kokarin da yake yi na ganin Kwalejin ilmi da ke Garin Zuba ta koma sashen da aka ware mata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel