EFCC na kokarin raba Patience Jonathan da makudan Miliyoyi

EFCC na kokarin raba Patience Jonathan da makudan Miliyoyi

- Hukumar EFCC na nema Kotu ta rufe wasu asusun Patience Jonathan

- Lauyoyin da ke kare Tsohuwar Uwargidar sun ce sam EFCC ba ta isa ba

- Yanzu haka Alkalin da ke shari’ar ya dage wannan kara sai wani makon

Mu na samun labari cewa Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu ya shiga Kotu inda ta ke kokarin raba Tsohuwar Uwargidan Kasar nan watau Patience Jonathan da makudan Miliyoyin da ta boye a bankuna sama da 15.

EFCC na kokarin raba Patience Jonathan da makudan Miliyoyi

EFCC na nema ta rufe asusun bankin Dame Jonathan

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin kasa zagon kasa tana nema Kotun Tarayya da ke Legas ta karbe duk wasu kudi na Mai dakin tsohon Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan da ke cikin wasu bankuna na kasar.

KU KARANTA: Ministar Buhari ta samu mukami a Majalisar UN

Sai dai Lauyoyin da ke kare Uwargidar tsohon Shugaban kasar watau Ifedayo Adedipe da Mike Ozekhome sun nemi ayi watsi da wannan roko na Lauya Rotimi Oyedepo na Hukumar inda su kace EFCC ba ta da wannan hurumi.

Yanzu dai Alkali mai shari’a ya dage karar sai mako mai zuwa watau a Ranar 23 ga wannan Wata na Junairu. Alkalin ya nemi a tabbatar da cewa babu inda ake shari’a game da kudin Matar tsohon Shugaban kasar a halin yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel