Bamu amince a kirkiri burtali domin makiyaya ba a gonakin mu - Dattijan jihan Benuwe suka fadawa Buhari

Bamu amince a kirkiri burtali domin makiyaya ba a gonakin mu - Dattijan jihan Benuwe suka fadawa Buhari

- Shugaba Buhari yi wata ganawa da dattawan jihar Benuwe a kan rikicin makiyaya a jihar Benuwe

- Sun ce basu yarda a kirkiri burtalai domin makiyaya ba a Jihar Benuwe

- Dattijan da suka halarci taron sun hada da David Mark da George Akume

Wasu dattawan jihar Benuwe da suka yi wata ganawa da shugaba Buhari a kan rikicin makiyaya da manoma da jihar Benuwe ke fama da shi, sun shaidawa shugaban cewar basu amince da kudirin kirkirar burtalai domin makiyaya ba a jihar.

Bamu amince a kirkiri burtali domin makiyaya ba a gonakin mu - Dattijan jihan Benuwe suka fadawa Buhari

Dattijan jihar Benuwe sun gana da Buhari

Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ne ya jagoranci dattijan ya zuwa fadar shugaban kasa domin tattaunawa a kan rikicin da jihar ke fama da shi.

DUBA WANNAN: Al'ummar garin Tunga a jihar Benuwe sun farkewa gwamna Ortom laya

Ministan harkokin noma da raya karkara, Audu Ogbeh, wanda kuma daya daga cikin dattijan jihar ne ya gabatar da kudirin kirkirar burtali mai girman hekta dubu goma domin magance rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Saidai, gwamnan Ortom, yayin ganawa da manema labarai jim kadan bayan fitowar su daga gana wa da shugaba Buhari ya ce basu da girman kasar da zasu kirkiri burtali domin amfanin makiyaya, yana mai cewa wasu jihohin z zasu iya yin hakan amma banda jihar Benuwe.

Ragowar dattijan jihar d da suka gana da shugaban sun hada da tsohon shugaban majalisar dattijai, Sanata David Mark, tsohon gwamnan jihar, George Akume da sauran su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel