Zaben 2019: Doguwa ya bukaci yan Najeriya da su marawa gwamnatin Buhari baya

Zaben 2019: Doguwa ya bukaci yan Najeriya da su marawa gwamnatin Buhari baya

- Dan majalisar wakilai na arewa maso yamma Doguwa ya yi magana akan nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari tun bayan da yah au karagar mulki

- Doguwa ya yi kira ga yan Najeriya da su ci gaba da hakuri da gwamnatin shugaba Buhari

- Ya bayyana cewa shugaban kasar ya yi kokari a shekarun da yayi yana mulki annan kuma bai taba gazawa ba wajen kara kaimi

Dan majalisar wakilai na arewa maso yamma Doguwa ya yi magana akan nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari tun bayan da ya hau karagar mulki domin inganta jin dadin rayuwarsu.

A cewar wani rahoto, Doguwa ya ce jam’iyyar All Progressives Congress APC ta jajirce don gyara al’amuran kasar, duk da halin da tattalin arziki ke ciki a yanzu.

Dan majalisan ya bayyana hakan a Kano lokacin wani shirin tallafi a mazabar Tudunwada/Doguwa.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama mutane 59 kan rikicin Wadata a Benue

Ya ce tare da goyon bayan yan Najeriya, shugaba Buhari ya yi kokari sosai sannan kuma zai kara kaimi domin tabbatar da cewa al’umman kasar sun ji dadin mulkin damokradiyya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel