Hukumar EFCC ta fara sabuwar yunkurin kwato dala miliyan $8.4m dake cikin asusun ajiyan bankin Patience Jonathan

Hukumar EFCC ta fara sabuwar yunkurin kwato dala miliyan $8.4m dake cikin asusun ajiyan bankin Patience Jonathan

- Hukumar EFCC ta kara shiga da karar Patience Jonathan a Kotu

- EFCC ta bukaci kotu ta ba ta izinin kwace makudan kudaden dake cikin asusun ajiyan kudin Patience Jonathan

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta fara yunkurin kwace kudaden dake cikin asusun ajiyan Patience Jonathan dake cikin bankuna 15.

Kudaden da hukumar EFCC ta ke son ta kwace daga asusun ajiyan, Patience Jonathan sun kai kimanin dala miliyan $8.4m wanda yayi daidai da naira N7.35bn a kudin Najeriya.

EFCC ta shigar da kara gaban alkalain babban kotun tarraya dake jihar Legas, Jastis Mojisola Olatoregun, akan neman izinin kwato kudaden.

Hukumar EFCC ta fara sabuwar yunkurin kwato dala miliyan $8.4m dake cikin asusun ajiyan bankin Patience Jonathan

Hukumar EFCC ta fara sabuwar yunkurin kwato dala miliyan $8.4m dake cikin asusun ajiyan bankin Patience Jonathan

Lauyan, Patience Jonathan, Mike Ozekhome (SAN), ya kalubalanci kudirin hukumar EFCC na kokarin kwace wa Patience Jonathan kudaden ta kotu inda ya bukaci alkali mai sharia yayi watsi da karar da EFCC ta shigar a kanta.

KU KARANTA : Fadar shugaban kasa ta mayar wa Fasto Tunde Bakare martani akan kakkausar suka da ya yiwa gwamnatin Buhari

Alkali mai sharia ya daga zaman sauraro zuwa ranar 23 ga watan Janairu na shekara 2018, kuma ya shawarci hukumar EFCC ta zo da shaidan da ya nuna ba a shari'an kudade dake asusun ajiyan Patience Jonathan, a gaban wata kotu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel